<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>82</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu Rasul, mai alheri,
 Ɗan Maryamu, mai nasiha,
 Haifuwarka ta ƙanƙanci,
 Ba mu ruhun jurewa.

[V2]
 2) Ko a can sakarkarinka,
 Ka zo ceton mutanenka
 Cikin duniya ta baƙunci,
 Karƃi mulkin zuciyarmu.

[V3]
 3) Kai mai fansar mutanenka,
 Mai yin nasara da mutuwa,
 Bar mu zauna kullayaumin
 Kurkusa da kursiyinka.

[V4]
 4) Kai mai ɗaukar wahalarmu
 Ka san dukan tunaninmu,
 Bar mu sa ido gare ka
 Don mu sami gaskiyarka.

[V5]
 5) Bishe mu, ya Ubangiji,
 Kau da dukan mugun nufi,
 Karƃi ranmu, mun roƙe ka,
 Don mu aika nufinka.</lyrics>
<title>Yesu Rasul, Mai Alheri LW82</title>
</song>